A ranar Talata ne wani dan uwan Sumayya Abubakar, Ibrahim Garba da masu garkuwa suka yi garkuwa da a kauyen Dauran, karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun saki Sumayya.
Idan ba a manta ba maharan da suka arce da Sumayya Abubakar, sun yi barazanar kashe ta nan da awa 24, idan ba a biya su diyyar naira miliyan 20 kafin su sake ta ba.
A wannan lokaci sun bada wa’adin awa 48 a cikin maganar da suka yi da mahaifin yarinyar mai suna Abubakar Yusuf.
Domin su tabbatar masa da cewa za su iya kashe Sumayya, maharan sun shaida wa mahaifin na ta cewa sun kashe wani matashi mai suna Surajo, wanda makwaucin Abubakar ne, kuma aka sace su rana daya da Sumayya din.
An sace Sumayya da Umar ne tun cikin watan Oktoba, tare da wasu mutane hudu, daga kauyen Dauran, cikin Karamar Hukumar Zurmi, a Jihar Zamfara.

Mahaifin Sumayya ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya na tsoron rasa ran ‘yar ta sa.
“Tun daga ranar da aka sace Sumayya har zuwa yau din nan, dukkan mu iyaye da dangin Sumayya ba mu cikin hayyacin mu.
“Irin mawuyacin halin da Sumayya ta ke ciki, dauke da ciki wata biyu a lokacin da aka sace ta, a cikin daji, ga rashin abinci da rashin ruwa, abin takaici da damuwa ne matuka.
“Wadanda suka yi garkuwa da ita su na cewa sai an biya diyyar naira miliyan 150 kafin su sake su. Daga karshe dai sai suka amince da miliyan 30, watau Sumayya naira miliyan 20, shi kuma Surajo naira milyan 10.
“A ranar da aka sako tagwayen nan, gida na ya shiga cikin wani mummunan yanayi, domin abinci ma bai iya ciwo gare ni. Sai da ta kai kadan ya rage zuciya ta ta buga.”
Abubakar ya shaida wa PREMIUM TIMES yadda aka yi kokari aka dan harhada kudade.
‘Na samu na yi magana da masu garkuwar a ranar Talata. Akwai wani dattijo mai suna Lawali Dauda, wanda tamkar uba ya ke a wurin mu. Tun da aka yi garkuwar shi ne ke tataunawa da masu garkuwar.
“Cikin taimakon Allah mun samu mun hada naira miliyan biyar. Daga nai sai Lawali ya kira su ya ce ga naira miliyan 5 an hada, ni zan kawo muku kudin a duk inda ku ke so na kawo muku.
“Amma da suka isa wurin, sai suka rike shi, tsammanin su mahaifin Sumayya ne su ke ta magana da shi kafin ya je wurin su.
“Dan achaba wanda ya kai Lawali wurin da suka ce a same su, ya ce da kunnen sa ya ji suna cewa ya ba su kudi, saboda sun san mahaifin Sumayya attajiri ne a yankin.
Mahaifin Sumayya ya ce sun rike dattijon nan Lawali, su ka ce shi ma ba za su sake shi ba har sai an biya su naira miliyan 50.
“A karshe dai mu ka ci gaba da ja-in-ja har suka ce idan ba mu biya naira miliyan 20 ba, to za su kashe Sumayya da wannan dattijon.
“To a lokacin ne ai suka shaida mana cewa sun kashe Surajo dan makwabci na, kuma suka rantse cewa idan ba mu biya su naira miliyan 20 nan da kwana biyu ba, to za su kashe Sumayya da dattijo Lawali.