Mahara sun kara kashe mutane 18 a Zamfara

0

An sake kashe akalla mutane 18 a lokacin da ’yan bindiga suka afka wa kauyukan Dutsen Kure da Manasa da ke cikin Karamar Hukumar Tsafe.

Wannan hari ya faru ne a ranar Sabuwar Shekara, kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu tabbacin faruwar lamarin.

Majiya ta ce mahara sun shiga kauyen Dutsin Kure suka kashe mutane tara, a kauyen Manasa ma suka sake kashe wasu tara.

An yi kisan, sa’o’i 72 bayan Gwamna Abdulaziz Yari ya kira taron gaggawa an batutuwan tsaro tare da shugabannin fannonin tsaro da sarakunan gargajiya na jihar.

Majiya ta kara cewa masu kai harin sun shiga kauyukan a kan babura dauke da muggan bindigogi, samfurin AK 47.

PREMIUM TIMES ta ji cewa makasan sun yi ta yin abin da suka ga dama a cikin kauyukan, har tsawon sa’o’i da dama, kuma su ka yi barazanar cewa duk wanda ya ko daga yatsa, to za su gama da shi.

Wani da ya tsere da kyar ya ce wasu sun gudu zuwa cikin jihar Katsina, wasu kuma musamnan daga Maradun sun gudu zuwa cikin jihar Sokoto.

Haka kuma maharan sun lalata rumbunan hatsi da dama.

Amma kuma Kakakin ’Yan sandan Jihar Zamfara, Shehu Mohammed, ya ce an tura ‘yan sTsafe
anda a wuraren da abin ya faru, har ma da inda ba a kai harin ba.

Kuma ya ce ana kokarin kamo makasan domin a hukunta su.

Idan ba a manta ba, a cikin makon da ya gabata ne Gwamna Yari ya ce ya goyi bayan a kafa dokar-ta-baci a jihar Zamfara.

Share.

game da Author