Wani babban lauya dan rajin kare hakkin dan Adam da ke zaune a Lagos, y amaka Rungunr Sojojin Najerya a kotu, ya na neman a hana su gudanar da atisayen ‘Operation Python dance a dukkan fadin kasar nan.
Lauyan mai suna Malcom Omirhobo, ya kai karar ce a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/01/2019, ta nuna cewa gudanar da atisayen tauyen hakki ne da kuma ‘yancin kowane dan Najeriya, da wanda ya yi korafi da ma wanda bai yi wa.
Malcom ya shigar da karar tare da hadin bakin lauyoyi da ke karkashin ofishin Malcom Omirhobo Foundation da Kwamitin Amintattun kamafanin lauyoyin gaba daya.
Cikin wadanda aka hada da su aka maka kotu, har da Ministan Shari’a, Majalisar Tarayya, Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda, da sauran shugabannin hukumomin tsaro.
Mai shigar da karar ya nemi a hana sojoji fara gudanar da shirin atisayen wanda Janar Tukur Buratai ya ce za a fara daga 1 Ga Janairu zuwa 28 Ga Fabrairu, 209.
Ya ce yin amfani da sojoji a cikin lamarin da ya shafi kasa a daidai lokacin da ake gudanar da zabuka a fadin kasar nan, ya kauce wa tsarin dimokradiyya, sannan uwa uba haramtacce ne a bisa tsarin dokar Najeriya a tafarkin dimokradiyya kuma zalunci ne.
Ya ce aikin ‘yan sanda ne kwantar da rikici na cikin farar hula aikin ‘yan sanda ne ba aikin sojoji ba ne.
Ya kuma nemi kotu ta tilasta wa ‘yan sanda karbar ragamar shirya tsaro a lokacin zaben 2019, kada a saka sojoji cikin aikin da ba na su ba.
Dama sai da jam’iyyar PDP ta yi korafi tun a ranar da aka bada sanarwar fara atisayen cewa an gwamnati shirya shi ne domin a yi magudi a zaben 2019, tunda dai har aka shirya atisayen a lokacin da za fara zabukan 2019.
Ba a dai sa a ranar da za a fara sauraren karar ba.