Lauyoyi sun bijire wa umarnin Kungiyar Lauyoyi, sun halarci zaman kotu

0

Lauyoyi a Babban Birni Tarayya, Abuja, sun halarci zaman kotu daban-daban, duk kuwa da umarnin da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta bayar cewa a kaurace tsawon kwanaki biyu.

NBA ta nemi lauyoyin su kaurace wa kotu ne saboda nuna rashin amincewa da dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen da Buhari ya yi.

Wakiliyar PREMIUM TIMES da ta halarci hedikwatar Babbar Kotun Tarayya da kuma Babbar Kotun FCT, ta ruwaito cewa lauyoyi sun je kotuna daban daban su na gudanar da sha’anin ayyukan su.

Ta shiga kotu da dama kuma duk ta same su cike makil da lauyoyin da suka je sauraren kararrakin da suke karewa.

Share.

game da Author