Kwamitin na ‘yan sandan SARS, ya fadi haka ne ta bakin shugaban su, Tony Ojukwu, a zaman da yay i jiya Laraba a Maitama, Abuja.
Hakan ya biyo bayan wani korafi ne rubutacce da ofishin lauya Sunny Olorunmola ya aika a madadin matar mamacin, mai suna Madam Okon, dangane da mutuwar mijin na ta.
Ta ce mijin na ta ya mutu ne a hannun SARS, bayan ya sha jibga da azabtarwa.
Matar ta ce an kulle mijin ta aka rika gasa masa azaba a ofishin SARS na Kaduna a karkashin wata ‘yar sanda mai suna Jummai.
Ta ce mijin ta ya shiga rikici bayan da aka balle gidan Dankwambo na Kaduna aka yi sata a ciki, a ranar 8 Ga Nuwamba, 2018.
Ta ce an sace manyan kyamarori na bidiyo har guda hudu.
Ta mijin ta da sauran masu hidima a gidan sun kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Kabala Costain, amma daga can sai aka yi caraf aka rike su.
“Washegari aka mai su hedikwatar ‘yan sanda ta kaduna, inda a ranar 13 Ga Nuwamba mijin ta ya fara rashin lafiya, aka garzaya da shi Asibitin Barau Dikko.”
Lauyan mai korafi Gloria Balkson, ta gabatar wa kwamiti rahoton da likitan da ya auna mamacin ya fitar a rubuce, inda ya ce:
“ Mamacin ya mutu ne sakamakon tsananin damuwa, azabtarwa, daukar cuta, zubar jini da kuma hujewa matattarar fitsarin sa.”
Haka likita Ayuba Godwin ya bayyana.
Ya kara da cewa cikin sa ya rika fitar da wani abu mai kama da garin barkono, kuma hanjin sa sun kumbura.
Lauyan ‘yan sanda ya tambaye shi yadda aka gudanar da binciken inda shi kuma ya amsa masa da cewa bangaren da ya jibinci gawarwaki ne na ofishin ‘yan sanda ne suka biya kudi aka yi awon.
Matar ta bayyana wa kwamiti cewa ta gane wani dan sandan SARS mai suna Baba Yakubu wanda ta ce shi ne ya rika gasa wa mijin ta bakar azaba.
Ta ce hatta ma ruwa da abinci sun hana mijin na ta ya ci ko ya sha.
Amma da shugaban kwamitin ya tambayai Baba Yakubu, sai ya musanta zargin da matar mamacin ta yi masa.
Ya ce shi ofishin sa a sama ya ke, ba shi ke aiki a kan kanta ba. masu aiki a kan kanta su ne ke da alhakin bai wa wanda ake tsare da shi abinci.
Kwamitin zai tura wa gwamnati rahoto domin a san matakin da za a dauka.
Discussion about this post