KURUNKUS: Bayan shekara 12, Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka

0

Idan ba manta ba anyi ta kai ruwa rana tsakanin mahukuntar kasar Amurka da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bisa rashin amince masa ya shiga kasar.

Wannan matsala dai ya samu asali ne tun a lokacin mulkin shugaban Kasa Olusegun Obasanjo inda shi da kan sa ya shirya masa wannan tuggu da hakan ya sa bai kara samun damar shiga kasar Amurka.

Wannan rashin shiga kasar Amurka da Atiku bai yi ba ya zamo masa kashin kifi a wuya domin duk lokacin da aka dauko wannan zance sai a danganta shi da irin watanda da karbar cin hanci da a ke zargin sa da hannu dumu-dumu a ciki, da aka shigar da wannan kara da tuhuma a kotun kasar Amurka.

Bayanai sun nuna cewa tabbas akwai hadin baki da kurda-kurda da tsohon shugaban kasa Obasanjo yayi domin ganin Atiku ya samu damar shiga kasar Amurka din sannan don a toshe bakin masu cewa bazai iya shiga kasar ba wai domin mahukuntar kasar na neman sa ruwa a jallo.

Bayan haka kuma tun a watan Disambar 2018 ne Amurka ta amince wa Atiku ya ziyarce kasar.

Tun bayan raba jiha da Obasanjo yayi da shugaba Buhari ya maida hankalin sa kacokan wajen ganin Atiku ne ya zama shugaban kasar nan a 2019.

Share.

game da Author