Kungiyoyin 20 Da Suka Fi Kashe Makudan Kudade Wajen Biyan Albashin ‘Yan Wasa

0

Shekara goma kenan Hukumar Kwallon Kafa ta Kungiyoyin Turai, wato UEFA ta na fitar da jerin sunayen kungiyoyin da suka fi kashe makudan kudade wajen biyan albashi.

Cikin wannan makon UEFA ta fitar da jadawarin jerin kungiyoyin da suka fi kashewa bayan kammala kakar wasan 2017.

Ga sunayen kungiyoyin nan fitattu 20. Lissafin ya fara ne daga kasa zuwa sama. Ma’ana, ta farko a sama, ita ce ta karshe, yayin da Madrid da Barcelona da ke can kasa, su ne na daya da na biyu.

An kididdige lissafin abin da kowace ta kashe a matsayin albashi ta hanyar lissafawa da kudin Yuro, wadda kowace Yuro miliyan 1 ta haura naira miliyan 400 na kudin Najeriya daraja.

20 AC Milan: €128m
19 Southampton: €131m
18 Leicester City: €132m
17 Crystal Palace: €133m
16 Wolfsburg: €139m
15 Roma: €145m
14 Tottenham €148m
13 Inter €155m
12 Atletico Madrid €178m
11 Borussia Dortmund €178m
10 Arsenal €234m
9 Liverpool €244m
8 Chelsea €256m
7 Juventus €264m
6 Paris Saint-Germain €272m
5 Bayern Munich €276m
4 Manchester United €306m
3 Manchester City €334m
2 FC Barcelona €378m
1 Real Madrid €406m

Share.

game da Author