Kungiyar Kwadago ta bada umarnin shirya fara yajin aikin da babu ranar dawowa

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta yi kwakkwaran kira ga daukacin ma’aikatan kasar nan da su fara shirin shiga yajin aikin da babu wanda ya san ranar komawa aiki.

Shugaban Kunguayar NLC ne Ayuba Wabba ya yi wannan umarni, tare kuma da yin kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta mika dokar karin mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000 ga Majalisar Tarayya dOmin a rattaba shi ya zama doka.

Wabba ya ce shekarar 2018 ta zama shekara mafi matsatsi ga ma’aikatan kasar nan saboda kin amincewa da dokar karin albashi mafi Kankanta zuwa naira 30,000.

Ya ce kungiyar kwadago da mambobin ta ma’aikatan fadin kasar nan, sun gaji da kwan-gaba-kwan-bayan da gwamnati ke yi wajen kin cika alkawarin ta na karin mafi kankantar albashi.

“Don haka mu na umartar ma’aikatan fadin tarayyar Najeriya da su shiga shirin fara yajin aiki wandab a a san ranar dawowar sa ba.

Ya ce hakan ya zama tilas idan aka yi laakari da yadda gwamnati ke jan-kafa ga lamarin na batun karin albashi mafi kankanta.

Wannan sabuwar barazana da kungiyar kwadago ta fito da ita a yau, ta zo ne jim kadan bayan da Kungiyar Gwamnoni ta fitar da sanarwar cewa gwamnoni ba za su iya biyan naira 30,000 a matsayin albashi mafi kankanta ba.

Share.

game da Author