Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, ta nuna rashin gamsuwa da irin yadda gwamnatin tarayya da gwmnatin jihar Zamfara ke nuna sassauci wajen gaggauta murkushe ‘yan bindigar da ke ta kashe jama’a da yin garkuwa da su a jihar Zamfara.
Jama’atu ta ce ta gaji da jin yadda a kullum idan an kai hari sai dai gwamnati ta ce ta yi Alla-wadai da masu kai hari.
Kungiyar ta ce ta na so ta ga an dauki kwakkwaran mataki wanda zai gaggauta kawo karshen wannan fitina.
A jiya Talata ne Jama’atu ta fitar da takardar nuna rashin jin dadi, wadda Babban Sakataren kungiyar, Khalid Aliyu ya sa wa hannu a Kaduna, ta na kuma mai kara cewa ta damu kwarai da sake famtsamar Boko Haram a jihar Yobe da Barno.
Ta nuna takaicin yadda aka yi sakaci aka bar al’ummar wasu yankuna na jihar Zamfara a hannun ‘yan bindigar da ke ta ci gaba da wulakanta su da taozarta rayukan bil Adam tare da kona dukiyoyi, sace musu dabbobi da kuma tarwatsa musu gidade da garuruwa.
“Shin don me kuma za a yi sakacin sake dawowar wannan kashe-kashe a Zamfara, Yobe da Barno?”
Daga nan sai Jama’atu ta yi kira da a gaggauta kafa binciken ainihin musabbabin kashe-kashen Zamfara, domin abin al’ajabi ne a ce jiha kamar Zamfara irin wannan bala’i na afkuwa haka, duk da alkawarin da gwamnatin tarayya ke yi a kullum cewa za ta shawo kan lamarin.
Daga nan ta yi wata kakkausar tambaya cewa, shin su wane ne wadannan da ke kashe jama’a haka? Me ya sa suke karkashe su? Daga ina suke? Me ya sa aka bar su har suka yi karfi haka? Don me ba za a iya kama su a hukunta su kuma a kawo karshen fitinar ba?
Ta yi kira ga limamai da su shiga addu’o’in neman Allah ya kawo karshen wadannan fitintinu.