Wata kungiya mai suna ‘African Centre for Media and Information Literacy’, ta bukaci Hukumar CCB ta bada bayanan ilahirin kadarorin da sabon Cif Jojin Najeriya, Ibrahim Mohammed ya mallaka.
A cikin wata takarda da AFRICMIL ta raba wa PREMIUM TIMES, ta hannun kodinetan kungiyar, Chido Onumah, ta ce kungiyar na da hakkinn sanin kadarorin da sabon Cif Jojin ya mallaka, kamar yadda Dokar 1999 ta ‘yancin bayyana wa al’umma bayanan jami’an gwamnati ta tanadar.
AFRICMIL ta nemi sanin kadarorin da ya mallaka shekaru hudu da suka gabata, da kuma wadanda ya mallaka har zuwa ranar da aka rantsar da shi, wato Asabar da ta gabata.
Dokar dai ta ce kowane ma’aikaci ko mai rike da mukami a Najeriya, tilas ne a duk bayan shekara hudu ya mika wa hukumar CCB bayanai na ilahirin kadarorin da mallaka kakaf, ciki har da kudaden da ya mallaka a banki ko bankuna.
Dokar ta kuma kara da cewa zai yi bayanin basussukan da ake bin sa, ko wanda ya ke bi, ko aro ko ginginar wata kadara da ya bayar ko ya karba.
An kuma gindaya sharadin cewa zai mika bayanan ilahirin dukiyar da ‘ya’yan sa wadanda ba su yi aure ba suka mallaka, matsawar dai ba su wuce shekara 18 a duniya ba.
Wadannan bayanin ne kungiyar ta nema a ba ta ta gani idan sabon Cif Jojin da Buhari ya nada bayan ya dakatar da Walter Onnoghen ko ya cika sharuddan ko a’a.
An dakatar da Onnoghen ne saboda zargin kin bayyana kadarorin sa.
A baya wannan kungiya ta sha aikawa da takardar neman bayanan kadarorin shugabanni daga hannun Hukumar CCB, amma ana yi mata walle-walle.
Wannan kwatagwangwama ce ta sa sai da kungiyar ta dangana da Majalisar Tarayya da kuma Babbar Kotun Tarayya wato Kotun Koli.
Discussion about this post