Ku daina yi mana shishshigi kan batun dakatar da Onnoghen – Najeriya ga Amurka da EU

0

Fadar Shugaban Kasa ta fitar da kakkausan raddi ga Amurka da Kungiyar Kasashen Turai cewa su daina yi wa Najeriya shisshigi da katsalandan a kan batun dakatar da Cif Joji, Walter Onnoghen.

Cikin sanarwar da Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar, duk da cewa Najeriya na neman hadin kan Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2019 cikin adalci da kwanciyar hankali, to kuma ba za ta lamunci wasu kasashe su rika yi mata katsalandan a harkokin da suka shafi cikin gida Najeriya ba.

Wannan tirka-tirka dai ta biyo bayan dakatar da Walter Onnoghen, Cif Jojin Najeriya da Buhari ya yi.

Dama kuma kwanki kadan kafin sannan Amurka da Turai sun jaddada cewa za su duba yiwuwar hana bizar shiga kasashen su ga duk wanda ya yi magudin zabe.

Sannan kuma sun nuna shakkun su dangane da tabbatar da sahihin zabe, ganin yadda aka dakatar da Cif Joji ana saura kwanaki kadan a gudanar da zabe da aka ta rurutawa ana cewa za a yi adalci.

Sanarwar ta ce duk da dai akwai fahimtar diflomasiyya a tsakanin kasashen, to Najeriya fa za ta iya gudanar da zaben ta ba tare da neman goyon bayan duk wata kasa ko kungiyar da kundin tsarin Najeriya bai tilasta cewa sai da sa hanunta ko goyon bayan ta za a iya yin zabe a Najeriya ba.

Kungiyar Kare Muradin Musulman Najeriya, MURIC ita ma ta shawarci Turai da Amurka cewa su daina shisshigi. MURIC ta ce domin ko a kasashen su ne ba za su amince a ce Cif Jojin kasashen su ya tara kudaden da ba a san ta inda ya same su ba. Ta ce su kwantar da hankalin su, gyara ne ake so a yi wa sashen shari’a tare da tsaftace shi.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce ta gayyato Tarayyar Turai domin ta sa ido wajen ganin yadda za a gudanar da zaben 2019.

Share.

game da Author