Kotu ta tsare wani da ya kashe saurayin tsohuwar matar sa

0

A yau Juma’a ne babbar kotun Makurdi jihar Benuwai ta gurfanar da Abunde Goja da laifin kashe saurayin tsohuwar matarsa.

Kotun ta kama Goja da aikata laifuka uku wanda suka hada da kisa, shiga kungiyar asiri da hada baki da wasu domin cutar da wani.

‘Yar sandan da ta shigar da karar Veronica Shaagee ta bayyana cewa Goja ya kashe saurayin tsohuwar matsarsa ne a gidan mahaifin Tsohuwar matar sa ranar 7 ga watan Janairu.

” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Goja ya dade da rabuwa da matsarsa amma bayan matar ta sami sabon saurayi ne Goja ya fara kishi.

” A dalilin wannan kishi ne Goja ya fara bibiyan wannan saurayi inda bayan dan wani lokaci ya hada baki da wasu ‘yan kungiyar asiri inda suka tare shi suka rika sarar sa da adda sannan suka watsa masa ruwan batir a kai.

Shaagee ta ce sun kama Goja da addan da ya yi saran, rigar sa da ya bata da jini da wasu makamai.

Ta ce tana rokon kotu da ta daga shari’ar domin ‘yan sanda su ci gaba da bincike.

Share.

game da Author