Kotun Majistare ta Osogbo, ta bada umarnin a ci gaba da tsare wani matashi mai shekaru 23, mai suna Peyemi Adeleke, bisa zargin sa da ake yi da satar dan kamfai na mata.
Adeleke ya musanta zargin da ake yi masa na cewa an same da da abin da ba na sa ba, mallakar wani.
Mai shari’a Mary Awodele, ya ce a tsare shi a kurkuku, saboda abin da ta kira girman laifin da ya aikata.
Mai gabatar da kara Jafani Mysilimi, ya ce Adeleke ya saci dan kamfan a ranar 21 Ga Janairu, da misalin karfe 1 na dare, a unguwar Agunwande, cikin Osogbo.
Mai shari’a ya ce dan kamfan na wata wata mata ce mai suna Gift Sunday.
“Jami’an ‘yan sanda sun sha wahala sosai kafin su samu nasarar karbo dan kamfan daga hannun sa. Daga nan muka kawo shi kotu.” Inji mai gabatar da kara.
An dage sauraren karar zuwa ranar 12 Ga Fabrairu. Kuma alkali ya hana belin sa.
RUWAN DARE
A kudancin kasar nan dai a yanzu satar dan kamfai na mata da kuma tsintar kunzugun da mata suka jefar a cikin bola, ta zama ruwan dare. Ana zargin cewa matsafa ne ke umartar a kai musu dan kamfai ko kunzugu su hada wa mutum wani asiri da shi.