Kotu ta bada belin Dino Melaye

0

A rabar Juma’a ne babban kotu a Abuja ta bada belin sanata mai wakiltar Kogi ta yamma sanata Dino Melaye.

Lauyan sanata Melaye, Mike Ozekhome ya nemi kotun ta yi haka a dalilin rashin lafiya da Melaye ke fama da shi.

Sharuddan belin da alkalin kotun Yusuf Haliru ya bada sun hada da gabatar da shaidu biyu dake da filaye a Abuja.

Sannan Melaye ya tabbata cewa da shi da shaidun biyu za su halarci kotu a duk lokacin da ta bukace su

Lauyan ya ce kama Dino da ‘yan sanda suka yi ba tare da ingantattun shaidu ko kuma hujjoji ba ya saba wa dokar kasa.

Shi kuwa lauyan dake kare ‘yan sanda Simon Lough yace sun kama Dino bisa ga bin doka.

Share.

game da Author