Ko Joshua Dariye ya bai wa Buhari gudummawar kudade da motocin kamfen daga kurkuku?

0

Tun a shekaranjiya, 2 Ga Janairu, 2019, kuma daidai karfe 11: 39 ne wani shafin soshiyal midiya na @LadiSpeaks ya bayyana sakon cewa tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye ya bai wa Shugaba Muhammadu Buhari gudummawar makudan kudade, da sunan gudummawa daga gidan kurkukun da ya ke tsare.

Dariye an ce ya bada kudaden a matsayin tallafin kamfen domin sake yin nasara a karo na biyu ga shugaba Buhari a zaben da za a gudanar a ranar 16 Ga Faburairu, 2019.

An ce ya bayar da motocin zagayen karakainar kamfen har guda 25 da kuma tsabar kudi naira miliyan 50.

Shafin na tweeter na yi karin haske da cewa ana wata gasar nuna bajintar wanda ya fi wani bai wa Tawagar Kamfen na Buhari gudummawar kudade da motoci.

PREMIUM TIMES ta gano cewa shafin twitter na @LadiSpeaks sahihiyar majiya kuma madogara ce, wadda ke da suna African giant-Ladi, mai kuma gudanar da bayar dahoro na shafukan internet na Google.

Ta na da mabiya har 62,500.

Cibiyar bin diddigi ta CCD ta nemi @LadiSpeaks ta ba su hotunan motocin da kuma hotunan sauran bayanan da za a tabbatar, amma ba ta bayar ba.

An tambayi Tawagar Kamfen na Buhari domin kare kan su. Amma sai Daraktan Yada Labari, Festus Keyamo ya ce shi ba shi da masaniyar wannan gudummawa, domin ba shi ne Daraktan Kula da Kayan Kamfen da Karbar Kudaden Gudummawa ba.

Shi ma kakakin Rotimi Amaechi, wanda shi ne Darakta Janar na Kamfen, wato Israel Ibeleme, ya karyata karbar kayan kamfen a matsayin gudmmawa daga Dariye.

Za ta iya yiwuwa wannan zancen ba gaskiya ba ne.

Sai dai kuma idan aka yi la’akari da yadda aka rika gasar sanar da bai wa Buhari gudummawa a sarari, za a iya cewa biri ya yi kama da mutum.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin samar wa Buhari kuri’a milyan biyar a Jihar Kano.

Ya yi wannan cika bakin ne kwanaki kadan kafin a same shi dumu-dumu da karbar toshiyar baki ta kashe-mu-raba daga ‘yan kwangila, wadda aka tona asirin sa ta wani faifan bidiyo.

Cikin watan Disamba, Hon. Abdulmumin Jibrin ya tura sako a shafin sa na tiwita cewa zai ba Buhari da Gwamna Ganduje na Kano, gudummawar motoci 150 domin karakainar yakin neman zaben 2019.

Shi ma wani mai suna Umar Bago daga jihar Neja, ya yi ikirarin bai wa kamfen din Buhari motoci 11.

Shi ma gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi sanarwar bada motoci masu dama domin tabbatar da nasarar kamfen din Buhari da Osinbajo.

BAYAN DARIYE SAI WA KUMA?

Tun bayan daure Dariye da aka yi a cikin watan Yuni, 2018, ana ta rade- radin cewa ya shiga tsamo-tsamo cikin harkokin siyasa daga gidan kurkuku. An tabbatar da cewa ya kira magoya bayan sa su zabi Buhari da gwamna Lalong na jihar Filato.

Sannan kuma an bada rahoton har fam na takarar sanata sai da ya yanka.

Shin me ya sa Dariye ne aka tsare, duk kuwa da sauran dimbin wadanda ke da alamar tambaya a kan su, musamman Rotimi Amaechi, Godswil Akpabio, AdamS Oshiomhole, Babachir Lawal, Kemi Adeosun, Minista Shittu da sauran na gaban-gashin Buhari?

Share.

game da Author