KEKE DA KEKE: Babu dangantaka na jini tsakanin Buhari da Amina Zakari

0

Idan ba a manta ba wasu da dama musamman ‘yan adawar siyasa sun yi ta tofa albarkacin bakin su bisa nadin Amina Zakari da akayi a hukumar Zabe a matsayin Kwamishina da zata kula da wuraren tattara sakamakon Zabe a 2019 a makonnin da suka gabata cewa an yi haka domin a saita wa jam’iyyar APC hanyar yin magudi ganin cewa ita dai Amina ‘yar uwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Sai dai kuma an gudanar da sahihiyar bincike domin gano wani irin zumunta ce ke a tsakanin Buhari da Amina.

Sakamakon wannan Bincike ya suna cewa babu dangantaka na jini dake a tsakanin su.

Ita dai Amina ‘yar gidan sarautar Kazaure ne shi kuma Buhari dan garin Daura ne. Amma abin da aka gano ya hada su shine tsohon sarkin Kazaure Husseini Adamu ya auri ‘ya’yar shugaba Buhari wanda shine mahaifin Amina Zakari, da ministan albarkatun ruwa na yanzu Suleiman Adamu da kuma sarkin Kazaure na yanzu Najib Adamu.

A dalilin haka shi kansa Buhari ya zauna a wannan gidan sarautar Kazaure saboda ‘yarsa da ke aure a gidan na tsawon lokaci.

Bayannan babu wani dangantaka na jini da ya hada su idan ba dalilin zaman ‘yar sa a wannan gida ba a matsayin matar sarkin Kazaure Marigayi Husseini Adamu.

Tun a lokacin da Buhari ke aiki a hukumar PTF, Amina da Suleiman suke aiki a tare da shi saidai ba kaman yadda ake yayadawa wai ‘yar uwar sa ne ba.

Share.

game da Author