Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke birnin Paris na kasar Faransa, Neymar Jr., ya bayyana cewa a daina saurin dora masa laifin yawan faduwa idan ana wasa.
Ya ce masu tsaron baya ne ke yawan takura masa, su na kayar da shi. Ya ce shi ma bada son ran sa ake kayar da shi ba, domin babu dan wasan da zai so a ce ana kayar da shi har ana ji masa raunin da zai zauna zaman jiyya, ba tare da buga kwallo ba.
Da ya ke magana da kafar yada labarai ta Canal+, Neymar ya ce idan mutum ya kalli abin da ya rika faruwa da shi sosai a lokacin Gasar Kofin Duniya da aka gudanar a Rasha, za a ga ba laifin sa ba ne ko da sau daya.
Ya ce ba daidai ba ne da ake cewa ya na saurin faduwa da gangan a cikin yadi na 18 na abokan wasa domin ya samu bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Da ya juya a kan yadda tsinci kan sa a rayuwa cikin birnin Paris, bayan sayen sa da PSG daga Barcelona a kan kudi fam milyan 222, Neymar yab ce ya dan sha wahala kafin ya saba da rayuwar birnin, amma dai yanzu ya zama dan gari, ya zama kunnuwan gari, kuma ya zama idon gari.
Discussion about this post