Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta kara jaddada cewa ba fa za su iya biyan naira dubu 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi ba.
Gwamnonin sun jajirce cewa ko ma sun fara, to tsarin ba zai dore ba, kuma yanayin da ake ciki ba yanayi ne da ya dace a yi karin ba.
Maimakon haka, kungiyar ta amince da cewa jihohi za su iya biyan naira 22,500 kadai a matsayin mafi kankantar albashi.
Sai dai kuma sun ce duk jihar da ta ga ita za ta iya yin kari don kan ta, to za ta iya karawa sama da naira 22,500 din da suka amince.
Gwamnonin sun kuma ce ba gaskiya ba ne da Kungiyar Kwadago ta ce wai ba su so su biya karin albashin.
Sun ce su na son biya, amma halin biya ne a yanzu ba su da shi, idan suka yi la’akari da adadin kason da suke karba na kudade duk karshen wata daga hannun gwamnatin tarayya.
Kakakin Yada Labaran Kungiyar Gwamnonin, Abdulrazak Bello Barkindo ne ya bayyana haka, a cikin wata takarda da ya aiko wa PREMIUM TIMES.