KAMFEN DIN BUHARI: Jaruman Kannywood sun fantsama birnin Kano

0

A yau Juma’a 25 ga wata ne jaruman fina-finan Kannywood suka fantsama cikin birnin Kano domin tallata shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa na APC.

‘Yan wasan sun saka kaya masu dauke da tambarin APC, da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari.

Jarumai irin su Alhassan Kwale, Adam Zango, Lawal Nuhu, Ibrahim Maishinku, Rabiu Rikadawa, Daushe da sauran su ne kan gaba wajen fita wannan gangami.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin matasa da Nasir Adhama ne ya shirya wannan gangami.

Suma wasu fitattun yan Kannywood din da ke bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP, ba a bar su a baya ba.

Tuni suka fito da nuna goyon bayan su da yin kamfen ga gwanin su wato Atiku Abubakar.

Share.

game da Author