Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai da takawaran sa Darius Ishaku na Jihar Taraba, sun yanke shawarar yin afuwa ga fitinannun mutanen da ke haddasa fitintinu a kan jiyakokin jihohin biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa an yi musu tayin afuwar ne a lokacin da jihohin biyu suka yi wani taron sha’anin da ya danganci tsaro a tsakanin jihohin biyu.
An gudanar da taron a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Wukari, Jihar Taraba.
Da ya ke karanta takardar da abin da sakamakon taron ya kunsa, bayan sun kammala rangadi a yankunan garuruwan Abako, Sai da Dogon-Gawa, Gwamna Ishaku ya ce an bada kofar wannan afuwa ne tun daga ranar da yayi jawabin, har zuwa karshen watan Janairu.
“Za mu yi afuwa ga batagarin da ke tafka laifuka, matsawar za su amince su daina su zama mutane nagari, sannan kuma su kawo makaman da ke hannuwan su. Idan suka yi haka, to za mu ba su aikin da za su rika yi su na dogara da kan su, tare da sake maida su mutanen kwarai a cikin al’umma.
“Duk wani mai laifin da kec son ya yi saranda, ciki har ma da wadanda a baya suka yi amma suka tayar da tubar su, to za su iya kawo makaman su ta hanyar tuntubar mu ko sarakunan gargajiya ko jami’an tsaro.”
Ya ce zaben 2019 ya kusa, don haka ya na son su gaggauta tuba tare da damka makaman su, domin a zamu zaman lafiya kuma a yi zabe cikin kwanciyar hankali lami lafiya.
Jihihin biyu dai su na fama da yawaitar fashi da makami, garkuwa da jama’a da hare-hare tsakanin matasan yankin, musamman a kan iyakar ta Benuwai da Taraba.
Discussion about this post