Hadaddiyar Kungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa mai suna CUPP, sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga matsawar dai Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa, Idris Ibrahim bai sauka daga aiki a ranar 15 Ga Janairu ba.
Tsari da dokar aiki ta gindaya cewa duk wanda ya kai shekaru 35 ya na aikin gwamnari, ko kuma ya shekara 60 a lokacin da ya na cikin aikin gwamnati, to ritaya ta wajaba a kan sa.
To a cikin wannan watan ne, a ranar 15 Ga Janairu, Idris zai cika shekaru 35 ya na aikin dan sanda, wanda kuma wajibin sa ne ya yi ritaya kenan.
Cikin makon da ya gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da shugaban na hukumar ‘yan sanda, wanda hakan ya haifar da rade-rashin cewa za a kara masa wa’adi.
CUPP ta ce ba ta amince a kasa wa Idris ko da kwana daya ba. Kuma idan aka kara masa za ta gudanar da zanga-zangar game-gari domin kin amincewa.
“jam’iyyun sun ce za su gudanar da zanga-zangar zaman dirshan ne a kofar hedikwatocin rundunar ‘yan sanda ta kowace jiha, har sai an fasa kara masa wa’adin.
Kakakin su Ugochinyere ya ce za a fara zanga-zangar ce tun daga ranar 15 Ga Janairu, matsawar aka ga Idris a sanye da kayan dan sanda.
Ya ce wa’adin sa ya kare tun daga 3 Ga Janairu, don haka kujerar kamar ta na a matsayin babu kowa a kan ta kenan a yanzu.
Sun yi amfani da sashen doka na 215(1), na 1999, suka furta cewa haramun ne Idris ya ci gaba da sa kayan ‘yan sanda tun daga ranar 3 Ga Janairu a ranar da wa’adin sa ya kare a aikin dan sanda.