Irin mulkin Abacha Buhari ya ke yi a Najeriya – Inji Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirya murdiyya a zabe mai zuwa.

Obasanjo ya kara da cewa Buhari yana mulki ne kamar yadda marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha yayi, wato mulki na dole ka bi ko ka kuka da kanka.

” Buhari yayi nasarar rudin mu mu yarda da shi a wancan lokacin, idan muka bari ya sake zura mu a wannan karon to lallai mun zama wawaye.

” Buba Galadima da shine ya fi kowa kusantar Buhari, sannan na gaban goshin sa ya fadi ba sau daya ba ba biyu ba cewa Buhari fa ba mutum bane mai yin nadama a rayuwa sannan bashi da tausayi kuma baya canja wa.

Obasanjo ya ce irin wannan hali na Buhari, hali ne irin wanda ‘yan Najeriya suka yi fama da a zamanin mulkin marigayi Abacha.

” Idan ba a manta ba a lokacin Abacha ya zagaye kan sa ne da wadanda ko ta halin kaka sai sun tabbata burin sa ya cika ko da ko za su ga bayan ka ne. A kwana a tashi Buhari ya fara zama haka.

Ya ce a yanzu haka Buhari da makarraban sa sun fara daukar masu kula da zabe domin karkata kuri’u domin samun nasara ko ta halin kaka a zabe mai zuwa.

” Wannan shine babban dalilin da ya sa ya ki saka hannu a sabon dokar zabe. Yanzu haka shi da makarraban sa suna nan suna tattara jami’an tsaron da za su yi musu aiki da jami’an tsaro da kuma wadanda za su rika coga musu kuru’i ko ta halin kaka don su yi nasara.

” Ina so su sani cewa muna nan mun gwaggwalo idanun mu sannan mun bibbi ta ko ina muna sanar wa mutane shirin su. Sannan mun sanar wa kasashen duniya da su sa ido domin abin da ake shirin yi kenan.

Share.

game da Author