INEC za ta raba katin rajista na PVC a wuraren rajista da mazabu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa za ta raba katin rajista na dindindin, wato PVC a wuraren da aka yi rajistar da kuma mazabu.

Acikin wani bayani da shugaban wayarwa da yada labarai na hukumar mai suna Festus Okoye ya fitar, za a fara raba katin ne daga ranar 16 zuwa 21 ga Janairu.

Ya ce za a rika raba su ne a wurare har 8,809 a fadin kasar nan, kuma har ranakun Asabar da Lahadi za a raba su.

Wadannan Katina su na daga cikin wadanda aka yi rajista har miliyan 14,283.734 daga ranar 27 Ga Afrilu, 2017 zuwa 31 Ga Agusta, 2018.

Don haka INEC ta ce ta bugo wa kowa katin sa, kuma ta rarraba su a jihojin da kowa ya yi rajista.
INEC ta ce amma daga ranar 8 Ga Faburairu, ba za a kara raba katin ba.

Hukumar ta yi kira ga duk wanda bai karbi katin rajistar sa ba, ya hanzarta zuwa ya karba.
Akwai masu rajista har milyan 84 kenan a kasar nan da ake sa ran za su fito su jefa kuri’a a zaben 2019.

Share.

game da Author