INEC ta gano mazabu 24 da zabe ba zai yiwu ba a Jihar Yobe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta gano wasu mazabu har 24 a Jihar Yobe, wadanda saboda matsala ta tsaro, zabe ba zai yiwu ac gudanar da zabe a yankunan ba.

Kwamihinan Zabe na Jihar, Ahmad Makama ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da juna a Damaturu, Jihar Yobe, a ranar Laraba.

Ya ce jami’an tsaro sun gano wasu yankuna a cikin kananan hukumomin Gulani, Gujba da Giedam cewa zabe ba zai yiwu a yankunan ba.

Makama ya ce INEC ta na tattaunawa da mazauna yankunan wadanda suka yanki rajisata domin sama musu mafitar yadda za a yi su yi zabe.

Ya ce INEC na kokarin tabbatar da cewa duk wanda ya yanki rajista ya yi zabe. Don haka ta na tuntubar dukkan jam’iyyun siyasa domin a cimma matsaya daya ta inda mutanen mazabun da abin ya shafa za su jefa kuri’ar su.

Ya ce akwai katin rajisata 69,000 da har yau ba a karba ba a jihar Yobe.

Ya yi kira ga masu katin da su garzaya su karbi abin su domin samun damar jefa kuri’a a wannan zabe mai zuwa.

A karshe ya bada tabbacin cewa akwai matakan tsaro sosai a sauran rmazabu 2.823 a fadin jihar.

Share.

game da Author