Akwai takaici abun da ya faru a baya a Majalisar Tarayyar Najeriya. Abun kunya ne ma, kwarai da gaske an zubar mana da mutunci a idon duniya saboda dole dabi’ar da ‘yan Majalisa suka bayyana ta shafi mutuncin talakan Najeriya domin wakilan da muka zaba da hannunmu ne a wajen kuma suka bayyana halayyar da muke gani akan teburin mai shayi da gidan kallon ball.

Tabbas a gidan kallon ball ne ake yiwa wanda baya goyon bayan wata kungiya ihu musamman idan wannan kungiya ta samu nasara akan wacce yake so. Misali, akwai wasan da ake kiran sa da ‘El’classico’ tsakanin kungiyar Madrid da Barcelona, a wannan wasa ne masu goyon bayan kungiyoyin guda biyu suke yi wa junansu ihu.
To wannan shine kwatankwacin abun da ya faru kenan a majalisar kasar mu. Wasu ‘yan majalisa sun yiwa shugaban kasa ihu, wasu kuma daga ciki suna ihun sai Buhari a lokacin kaddamar musu da budget. Wannan ba shine aikin da muka tura su ba kwarai da gaske.
Akwai babbar alaqa tsakanin cigaban kasa da ingancin majalisar kasar saboda duk inda wakili yake a siyasa yana da alaka da lalacewa ko cigaban wadanda yake wakilta. Shiyasa kullum muke gani a tashoshin duniya ana hasko mana majalisar kasa domin daga abun da yake faruwa ne a cikinta zaka iya hango abun da yake faruwa a kasar gaba daya.
Bayan Najeriya ta samu ‘yancin kai an shiga cikin rikicin mulki a kasar a sakamakon rashin hadin kai a cikin ‘parliament’ saboda wani bangare yana da gilli a zuciyarsa don haka ba zai iya hakura ba ya bar wani bangaren ya zama mai rinjaye a cikin gwaunati.
Hakan ne yasa a karshe aka shigo da juyin mulki wanda shine haifar da duk ragowar juyin mulkin da suka biyo baya kuma ya rusa amincin da yake tsakanin bangarori guda biyu na kasar Najeriya.
Duk sanda majalisar kasa ta shiga rikici na babu gaira-ba-saba, to lallai talaka ya shiga cikin rikici shima.
Adawa mai tsafta tana cikin kyawun siyasa, babu wanda yake inkari akan wannan tun daga karamar hukuma har zuwa gwaunatin tarayya amma adawa irin ta jagaliya bata da gurbi a siyasa. Kamar yadda na fada a baya, cigaban siyasar ku yana da alaqa da ingancin wakilanku.
Ma’ana dai, gwargwadon lalacewar dabi’unsu haka kuma zaku kasance koma-baya. Aikin majalisa wakilci ne ta hanyar yin dokar da ta dace da cigaban kasa don haka ne ma ake bawa talakawa shawara da su san wadanda zasu tura can idan ba haka ba za a cigaba da ganin ba daidai ba saboda wadanda suke wakiltar ra’ayinku sun kasa yin ‘bargaining’ da abokan aikin su wajen shigar da kudirin ku, sun koma yi wa juna ihu kamar a gidan kallon ball din Arsenal ko Manchester.
Allah ya shiryar damu.
Discussion about this post