Ina tare da hukuncin da a aka yanke na babu dan takara a APC a jihar Zamfara – Kabiru Marafa

0

Sanatan dake wakiltar jihar Zamfara a majalisar dattawa Kabiru Marafa ya yaba wa hukuncin da kotu ta yanke na kin amincewa da dan takara koda daya ne na jam’iyyar APC daga jihar.

Idan ba a manta ba hukumar Zabe ta sanar cewa ba za ata amince da dantakara ko daya ba daga jam’iyyar APC a jihar zamfara cewa jam’iyyar ta kasa gudanar da zaben fidda gwani har lokacin da aka dibar mata ya wuce.

A jerin sunayen da hukumar ta fitar babu dan takara ko da daya ne daga jihar Zamfara da ta saka.

Sanata Marafa ya ce abinda hukumar ta yi da hukuncin kotu shine ya fi dacewa da jam’iyyar APC a jihar.

Sai dai kuma ana haka ne Kotu a garin Gusau ta yanke hukuncin cewa a saka sunayen ‘yan takara na jam’iyyar APC a cikin jerin wadanda za su fafata a zabe mai zuwa.

Gwamnan jihar AbdulAziz Yari ya yaba wa wannan hukunci da kotun jihar ta yanke sai dai kuma sanata Marafa ya ce ba zai amince da wannan hukunci da aka yanke ba.

Marafa ya ce ko da ko karfin sa zai kare ne zai tabbata hakan bai tabbata ba domin idan ma aka nemi amfani da wannan hukunci na kotun Zamfara zai garzaya kotun daukaka kara.

Share.

game da Author