Ina rokon hasalallun ‘yan jam’iyyar APC kada su yi mana Zagon Kasa a jihar Barno – Kashim Shettima

0

Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima ya roki hasalallun ‘yan jam’iyyar APC da su yi hakuri da kurakuran da a tafka musamman a wajen zaben fidda gwani na jam’iyyar su dawo a hada kai domin samun nasarta a zabuka masu zuwa.

Shettima ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da Kamfen din Jam’iyyar APC da aka yia agarin Maiduguri.

” A matsayin ka na dan jam’iyya, gatan ka shine irin gudunmawar da kaba jam’iyyar har aka yi nasara a zabe. A misala Idan aka samu matsala a kananan hukumomin MMC, Chibok, Hawul, Askira Uba da Biu, har PDP ta yi nasara a wadannan wurare, ka ga mutum bashi da ta cewa kenan idan har jam’iyyar ta yi nasara daga baya. Dole ya zama saniyar ware. A rika yi ba bashi.

” Sannan kuma ku sani mutane ba za su iya hakurin kana ce musu su zabi wannan jam’iyyar a nan ba wancan a can. Idan mutum yayi wa jam’iyya zagon kasa ya sani zai bayyana karara. A gani na taimakawa wanda baka ga maciji da ne ya fi dacewa domin idan yace za ak iay bugun kirji kace kai kataimaka masa yayi nasara.

” Ina rokon ku da kuyi hakuri a manta da baya. A hada kai ayi aiki tare don ci gaban jam’iyyar APC da samun nasarar ta a zabuka masu zuwa.

Share.

game da Author