Ina nan tare da Atiku da Obi daram a PDP – Ekweremadu

0

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa ba ya tare da PDP.

A cikin wani bayani da ya watsa a shafin sa Facebook, Ekweremadu ya ce duk karya ce ake yi masa cewa shi yanzu bad an PDP ba ne.

Ya ce bai ga dalilin da zai fice daga PDP ba a yanzu a lokacin da tauraruwar jam’iyyar ke kara hasken sake lashe zaben 2019, tunda dai har bai fice ba a 2015 a lokacin da harken tauraron jam’iyyar ya dishe har ta fadi zabe.

An rika yada ji-ta-ji-ta ne kan Ekweremadu, ganin cewa tun bayan zaben fidda-gwani ba a sake jin sa ba, tun bayan da Atiku ya fitar da Peter Obi a matsayin mataimakin sa na takarar zaben 2019.

An ce Ekweremadu ya yi tunanin shi ne Atiku zai dauka, ko kuma a matsayin sa na mafi babban mukami a cikin al’ummar kudu-maso-kudu, to idan Atiku zai fitar da mataimaki daga yankin, ya kamata a ce ya tuntube shi.

A safiyar yau Litinin, Ekweremadu ya fitar da bayanin cewa ya na nan ya na aiki tukuru tare da Peter Obi domin tabbatar da cewa PDP ta kayar da APC a zaben 2019 mai zuwa a cikin watan Fabrairu.

Daga nan sai ya ce magoya bayan PDP su yi watsi da duk wata farfagandar siyasa da ake yi masa, domin ya na nan ya na zaman taruka ba daya ba, ba biyu ba, tare da Peter Obi da shugaban kamfen na yankin Kudu mason Gabas, Peter Omahi, domin a kayar da APC.

Ekweremadu na takarar sake dawowa majalisar dattawa a Shiyyar Enugu ta Yamma a karkashin jam’iyyar PDP.

Share.

game da Author