Ina nan gadagau da karfi na sannan cikin koshin lafiya – Inji Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa yana cikin kuzari da koshin lafiyan da zan mulki Najeriya a karo na biyu.

Kadaria ta shirya wannan taro ne da ta yi wa suna ‘Yan Takara’ domin mutanen Najeriya su samu daman ganawa da ‘yan takarar su sannan su iya yi musu tambayoyi game da kasa Najeriya da irin shirin da kowa yayi wa kasar idan ya samu nasara a zabe mai zuwa.

Buhari tare da mataimakin sa Yemi Osinbajo su halarci tattaunawar bainar jama’a da fitacciyar ‘yar jarida Kadariya Ahmed ta shirya.

Buhari ya fadi cewa ba kamar yadda mutane ke ta yayadawa cewa wai bashi da koshin lafiyan da zai iya mulkar Najeriya a karo na biyu ba haka bane.

” Ina so ku duba yadda na yi ta zazzagaya filin taron kamfen din da muka yi a jihar Kogi ina gaisawa da mutane. Sannan kowa ya ji yadda na zakalkale ina lissafo wa dubban mutanen dake wannan fili irin ayyukan da muka yi tun bayan hawan mu a 2015.”

Share.

game da Author