Illar wanke gaba da sabulu ga mace – Malama Murna

0

Ma’aikaciyyar asibitin Major Ibrahim Abdullahi dake sabon gari Zariya jihar Kaduna, Murna Musa ta yi kira ga mata da su guji amfani da sabulu wajen wanke gaban su.

Murna ta ce yin haka na da matukar illa domin yana kawo cututtuka da dama.

Ta ce mace zata iya wanke gabanta da ruwa mai tsafta kawai.

Daga nan ta kuma yi kira ga mata da su daina cusa yatsa ko kuma yatsu a gabansu.

Ta ce shima yin haka na sa a kamu da cututtuka musamman idan hannun mutum bai da tsafta.

Share.

game da Author