Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya yi kira ga mutanen Najeriya da su bude kunnuwar su bibiyu su saurare shi cewa sufeto janar din ‘yan sandan Najeriya Idris Ibrahim ya na bibiyar rayuwar sa kowa ya sani.
Saraki ya fadi wa manema labarai haka ne a ofishin kamfen din jam’iyyar PDP a garin Abuja cewa duk abinda ya same shi Sufeto Idris ne ya kitsa kuma shine sanadi.
” Gaba daya yanzu abin ya fi karfin a zuba ido, ya kai ga ana bi na da mutane na har gidajen mu ana bugewa. An bi har unguwar mu na gado, na Iyaye da kakanni wato rukunin gidaje da ke Agbaji dake Ilorin ana bugewa sannan a na rugurguza musu sana’o’i.
” Abinda na gani ya tada min da hankali maruka domin ana yin wannan mummunar abu ne a gaban jami’an tsaro wato jami’an ‘yan sanda. Hasali ma sune suke raka wadannan matasa su aikata haka.
” Ina so kowa ya sani harda kasashen duniya da suka zuba ido don ganin yadda siyasar 2019 zai kasance a Najeriya cewa wannan karon fa abin na neman ya canja zani. Tun yanzu su fara ganin irin yadda jam’iyyar APC mai mulki ke so ta yi koda karfin tsiya ta zarce a kujerar mulki.
” Ina kira ga mutane su bude idanun su su karkato da hankulan su, su yi tir da irin wannan abu da ‘yan sanda suke yi wa ‘yan siyasa a kasar nan musamman mu da ba jam’iyyar daya muke ba da gwamnati mai ci.