Idan Buhari na so ayi tashin hankali ne, ya sani a shirye muke – Inji Secondus

0

Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shirya gwabzawa da su idan rikici ya ke so a yi kuma ya sani cewa a shirye suke game da binciken alkali Onnonghen da ake shirin yi.

Secondus ya ce shirin gurfanar da babban alkali Walter Onnoghen da gwamnatin Buhari ke so tayi farautar Alkalai ne domin ana so ko da karfin tsiya Buhari ya zarce.

” Idan rikici yake so ya sani a shirye muke.” Inji Secondus.

Secondus ya bayyana wa dubban magoya bayan jam’iyyar PDP hakan ne a garin Jos a wajen kamfen din dan takarar Shugaban kasa Atiku Abubakar.

A nashi jawabin a wajen taron Atiku ya ce zai tabbata zaman lafiya na dindindin ya tabbata a jihar Filato.

Ya kara da cewa zai maido wa jihar martabarta da mulkin APC ta goge a idanun duniya.

Haka kuma gwamnonin yankin Kudu Maso Kudu sun gargadi Buhari da ya yi watsi da shirin gurfanar da Alkali Walter Onnoghen, sannan sun yi kira ga alkalin da kada ya halarci zaman kotun da’ar ma’aikata CCT da take bukatar ya bayyana a gabanta domin kare kan sa bisa wasu laifuka da ya aikata na boye wasu daga cikin kadarorin sa a lokacin da ya ke bayyana abubuwan da ya mallaka.

Gwamnonin sun tsayar da wannan shawara ne a taron gaggawa da suka yi a garin Abuja, inda suka ce ana yi wa babban Alkalin bita da kulli ne.

Sai dai kuma gwamnan jihar Edo bai halarci wannan taro ba ganin shi dan jam’iyyar APC ne duka da dan yankin kudu maso kudun ne.

Duk da wannan barazana da gwamnonin suka yi bai hana gwamnati ci gaba da shirin gurfanar da wannan Alkali ba.

Da yawa daga cikin mutane sun soki wannan hukunci da gwamnonin suka dauka inda suka ce ai shi Onnonghen ba shafaffe da mai bane cewa idan har mutane irin su Saraki, da wasu manyan kasar nan za su bayyana a CCT din ba su ga dalilin kin haka da suke so shi alkalin ya yi ba bayan kuma doka ce shima ya karya.

Alkali Onnonghen, a yammacin Lahadi kuma ya fito karara inda ya karyata labarun da wasu jaridu suka dauka wai gwamnati ta yakice jami’an tsaron dake gadin sa.

Onnonghen, ya ce masu tsaron sa na nan daram tare da shi ba kaman yadda ake ta rade radi ba.

Ana sa ran a yau Litinin ne Onnonghen zai bayyana a gaban hukumar CCT domin amsa tuhumar da ake masa na kin bayyana duka kadarorin sa a lokaci da ya kama aiki.

Share.

game da Author