Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta fara horar da sabbin ma’aikata 4,650 da ta dauka aiki.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar, Bisi Kazeem ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an sanar da dukkan wadanda aka dauka aikin ta hanyar tura masu sakwanni a E-mail din su.
Kazeem ya ce tuni an fara ba su horon a wurare daban-daban a cikin kasar nan.
Ya ce ana bai wa wasu horon a Enugu, wasu a Jos, wasu a Kontagora.
Ya kuma kara da cewa ana ba su horon ne inda za su shafe tsawon watanni shida ana horas da su.
Discussion about this post