HARKALLAR BANKIN HABIB: Atiku ya karyata hannu a durkushewar bankin

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar Atiku Abubakar ya karyata zargin da gwamnatin Buhari ta ke yi masa cewa wai da shi aka yi watandan kudaden da yayi sanadiyyar rugujewar bankin Habib.

Idan ba a manta ba Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana wa manema Labarai cewa da zarar dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dawo kasar nan daga balagoron sa a kasar Amurka zai fuskanci matsananci tambayoyi daga hukumomin Najeriya.

Lai Mohammed ya kara da cewa, zuwan sa kasar Amurka bai dada gwamnatin Najeriya da kasa ba sai dai ya tunasar da mutane cewa lallai gwamnati basu so haka ba domin har shawara suka aika wa kasar Amurka din da kada su barshi ya shiga kasar.

” Wai don ya tafi kasar Amurka, wannan hukuncin kasar ne amma Atiku ya sani cewa da zarar ya dawo kasar nan zai fuskanci hukumomin domin amsda tambayoyi game da wasu kudade har naira miliyan 150 daga tsohuwar Bankin Habib.

Ya ce a ranar 13 ga watan Janairun 2009, Atiku ya karbi naira Miliyan 150 a wannan banki da duk yana daga cikin dalilin da yasa wannan banki ta ruguje.

“Idan ya ga dama ya ci gaba da zama a kasar Amurka, kai suma bashi katin zam na dindindin, amma fa ya sani cewa da zarar ya dawo kasa Najeriya gwamnati na nan tana jiran shi ya zo yayi bayanin wannan kudi sannan ya fadi inda suke. Kuma ya sani cewa zabe fa ba a Amurka za ayi ba, a Najeriya za ayi kuma ya sani zai sha kasa.

A martani da ya maida game da wannan zargi, Atiku ya kara da cewa yin haka wani salo ne da gwamnatin Buhari ta kirkiro domin jikin su kaf ya riga ya yi la’asar da irin dandazon mutanen da ke mara mana baya da shirin kifar da wannan gwamnati.

Atiku ya ce an dade ana so a ga bayan sa, amma hakan bai yiwu ba.

” Yau a kikrkiro wannan gobe a kirkiro wancan duk domin a kala mini wani abu amma duk da haka an kasa samu abu daya da za alika min har yanzu. Abin kunya shine har bibiyan kasar Amurka suka rika yi wai don su hana ni shiga kasar kafin in tafi.

” Ko shakka ba ni shi koda ko na sekon daya ne cewa yanzu sun fada cikin ribibi da fargaba. Su fito a fafata idan ba tsoro suke ba. Idan maganar nasara ne a zaben 2019, wannan kamar anyi an gama ne domin Buhari ya yi shirin shan kayi a zaben.

” Muna nan za mu fitar wa ‘yan Najeriya da irin tabargazar da aka tafka a gwamnatin Buhari dalla-dalla nam ba da dadewa ba.

Share.

game da Author