Gwamnatin Barno ta dauki mafarauta da ’yan tauri farautar Boko Haram

0

Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta tattara mafarauta da ‘yan tauri wadanda za a ba horon shiga aikinn karfafa tsaro.

Gwamnan ya fadi cewa sojoji ne za su bai wa wadannan mafarauta za a yi musu horo na gaggawa kafin a tura su ayyukan gadi da sa-ido a cikin yankunan birnin Maiduguri da kewaye.

Ya furta haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin Kwamandan Zaratan Operation Lafiya Dole. Benson Akinroluwo, wanda ya kai masa ziyara.

Gwamnan ya kara da cewa wadannan mafarauta an tattara su ne a wasu wurare na sirri a yayin da a yanzu haka gwamnati na kokarin ganin ta tanadar musu da dukkan kayayyakin aikin da ya wajaba su tanada.

“Mu ma nan da ‘yan kwanaki kadan za mu kaddamar da zaratan mafarauta da ‘yan tauri da ‘yan bijilante wadanda za su taimaka wajen dakile ta’addanci a fadin jihar nan.” Inji Shettima.

“ Mun kuma tanadar musu motocin sintiri har 30 domin gudanar da ayyukan sun a karfafa tsaro.

Ya ce za su karfafa ayyukan su ne a cikin kwaryar Maiduguri da kewaye, musamman ganin cewa ga zabe ya kawo kai, ya zama wajibi ga gwamnati ta kara karfafa tsaro.

Gwamnan ya jaddada wa kwamandan cewa jihar sa za ta ci gaba da bai wa sojojin da ke bakin daga goyon bayan ganin an kawar da ta’addanci a jihar.

Kwamandan ya shaida wa Gwamna cewa shi ba bakon Maiduguri da jihar gaba daya ba ne, domin ya taba yin aiki a bataliya ta 212 a jihar Barno.

Share.

game da Author