Gwamna Lalong ya yi wa Ahmed Musa Ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar sa

0

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya mika Ta’aziyyar sa ga dan wasan kwallon Najeriya, Ahmed Musa a dalilin rasuwar mahaifiyar sa Sarah Moses.

A sakon Ta’aziyyar da gwamman Lalong ya rubuta a shafin sa ta tiwita, Lalong ya ce
” Rasa mahaifiya abune mai ciwon gaske. Muna taya Dan uwan mu Dan Jihar mu Ahmed Musa juyayin rasuwar mahaifiyar sa Sarah Moses. Muna fatan Allah ya Kara masa hakura da mu baki day.” Inji gwamna Lalong.

Ahmed Musa na buga wasan kwallon kafa a kasar Saudiyya.

Share.

game da Author