GUMURZU: Sojoji sun kwato garin Baga daga hannun Boko Haram

0

Gumurzun fadan kwato garin Baga daga hannun Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa ran sojoji biyu, da kuma kakkabe ‘yan ta’adda masu yawa.

Kakakin Yada Labarai na Jojojin Najeriya, Burgediya Janar Usman Kukasheka, ya bayyana cewa an kwato Baga daga hannun Boko Haram.

Ya kara da cewa sojojin Najeriya sun nuna juriya da kishi kuma suka yi nasarar kakkabe Boko Haram masu yawa.

Duk da dai bai ambaci adadin wadanda aka kashe din daga Boko Haram ba, Kukasheka ya kara da cewa sojoji na ci gaba da bin sauran wadanda suka tsere cikin daji.

Baga gari ne mai matukar tasirin hada-hadar kasuwanci wanda Boko Haram suka ci da yaki kwanan nan.
Kukasheka ya tura hotunan sojojin Najeriya cike dankam a garin Baga, wasu ma a tsaye bakin Barikin Sojojin da ke garin.

Kafin wannan sanarwa da kuma hotunan da Kukasheka ya watsa, sojoji sun sha musanta cewa Boko Haram sun ci garin Baga da yaki, sun kori sojojin Najeriya da na Kasa-da-kasa.

Ya ce an samu wannan nasara ce tare da hadin kan sojojin sama wadanda suka rika yi wa Boko Haram ruwan wuta daga sama tare da jefa musu bama-bamai.

Share.

game da Author