Goni, Wampana sun koma APC daga PDP

0

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Barno da ya hada da Barno da Yobe na yanzu Mohammed Goni ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Goni ya bayyana haka ne a fadar shugaban Kasa bayan ganawa da yayi da shugaba Muhammadu Buhari wanda Sanata Ali Ndume ya jagoranta.

” Na san shugaba Buhari sosan gaske domin a lokacin da yake gwamna a yanki Arewa maso Gabas, ina sakataren karamar hukuma.

Bayan yayi gwamna a 1979-1983 ya sake takara a 2011. Sannan ya taba zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar UNPP kafinnan ya koma PDP. Goni ya ce tabbas yana da yakinin cewa Buhari mutum ne mai cika aiki.

Daga jihar Adamawa kuma, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar, sanata Paul Wampana shima ya sauya sheka zuwa APC din duk a yau.

Share.

game da Author