A hira da gwamnan jihar Kaduna yayi da Talabijin din Channels ranar Alhamis ya bayyana cewa taron PDP da aka yi a Kaduna ranar Talatar da ta gabata bai hana shi barci domin kuwa an san jam’iyyar da yin hayan mutane idan zasu yi gangamin su.
Idan ba a manta El-Rufai ya taba sukar jam’iyyar da irin wadannan kalaman bayan taron jam’iyyar a garin Sokoto inda ya ce mafi yawa daga cikin wadanda suka halaeci taron hayan su aka yi daga kasar Nijar.
Bayan nan ya masa tambaya game da kushe zabin mace da yai a matsayin mataimakiyar sa da fitaccen malami Sheikh Gumi yayi cewa bai dace ba yayi haka a siyasance.
” Bana so in cika yin magana game da Sheikh Gumi, amma abinda nake so ya sani sannan kowa ya sani shine, shi Gumi ba dan siyasa bane, harkar sa kaf ba ta siyasa bace a dalilin haka ba zai iya gane lissafin siyasa ba. Mune muke siyasa kuma mun fishi goge wa a wannan harka saboda haka ya dai na yin ganganci a abinda da bai sani ba.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a iya binciken da yayi tun bayan hawan sa karagar mulkin jihar Kaduna, ya gano cewa ashe jam’iyyar PDP bata taba cin zaben gwamna ba a jihar.
“ Ai ni taron PDP da suka yi a Kaduna bai dada ni da kasa ba ko kadan domin hayan mutane suka yi, kuma haka suke yi.
“ Duk da ina so in yi nasara a zabe mai zuwa dole in yi taka tsantsan wajen yanke hukunci a kan abinda na sa a gaba.
Discussion about this post