A sanarwar da kwamishinan yada labaran jihar Kano Garba Mohammed ya fitar ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta soke kwangilolin da ta ba kamfanin Tiamin mallakin Amin Mohammed da shine ya rika daukar gwamnan jihar a daidai yana mika masa daloli na cin hanci shi kuma yana karkacewa ya na zura su a aljihun jamfar sa.
Garba ya ce gwamnati ta yi haka ne ganin kamfanin bata birge a aikin ta.
Idan ba a manta ba a kwanankin baya ne aka bankado wani bidiyo dake nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje na karbar cin hancin daga hannu dan kwangila har sau biyu.
A bidiyon, Ganduje ya rika karkacewa yana zura daloli a aljihan sa.
Majalisar jihar ta nemi ta binciki wannan harkallar amma kotu ta dakatar da ita.
Shima kan sa shugaban Kasa Muhammadu Buhari da aka tambaye sa ko menene ya sa bai ce komai ba akai, sai yace ai hakan ba hurumin sa bane. Majalisar jihar sa ce za ta binciki haka da kuma kotu.
Discussion about this post