EMILIANO SALA: Har yau ba a fidda ran nemo dan wasan Cardiff City da jirgin da ya ke ciki ya bace ba

0

An shiga rana ta uku kenan ana neman dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City da ke Ingila, wanda su biyu shi da matukin jirgin da ya ke ciki suka salwanta bayan sun tashi sama.

Dan wasan Leganes Diego Rolan ya bayyana yadda dan wasan ya tura wa wani abokin sa sakon ‘tes’ kafin jirgin na su ya bace da su.

Cardiff City ta sayi Sala fam milyan 15, daga kungiyar Nantes ta Faransa.

Jirgin da aka dauka shata domin kai shi birnin Cardiff daga Nantes ya salwanta bayan na’urar kallon duk inda jirgin sama ke tunkara ta daina hangen jirgin da ya ke ciki.

Shi kadai ne aka dauko a ranar Talata, daga shi sai direban jirgin.

An ce an daina ganin jirgin tun bayan da ya gitta a sama gabar ruwa ta Guernsey, da ke kan iyakar Faransa da Ingila.

Har zuwa yau duk kokarin da ake yi domin gano su ko gano inda jirgin ya yi hadari, abin ya ci tura.

Iyayen sa da ‘yan uwa da abokan arziki har da dimbin ‘yan kwallo na duniya, duk hankulan su ya tashi.

Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City ita ma ta yi matukar firgita, kuma ta shiga jerin wadanda ke fatan cewa Allah ya sa su na nan da ran su da lafiyar su.

Share.

game da Author