Duk wanda aka samu yana taimakawa Boko Haram zai dandana kudar sa – Rundunar ‘Operaton Lafiya Dole’

0

A ranar Alhamis ne rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ta gargadi mazauna garin Maiduguri da kauyukan jihar Barno da su daina yi wa sojiji rufa-rufa game da ayyukan Boko Haram a yankunan su cewa duk wanda aka samu na haka zai dandana kudar sa.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ya sanar da haka inda ya kara da cewa za su hukunta duk wanda aka samu yana wani hulda da ‘yan ta’addan ko ta wani hali ne.

Nwachukwu ya ce aya zama dole a fitar da wannan gargadi ganin cewa ana samun rahotanni cewa wai Boko Haram din da yi wa wasu kauuyuka barazanar kawo musu hari da kuma tilasta wa mutane su basu shiga kungiyar.

Ya roki mutanen irin wadannan garuruwa da su tabbata sun ba da gudunmawa wajen tona asirin wadannan mutane.

Idan ba a manta ba a Laraba ne Sojojin Najeriya suka tsare babbar hanyar shiga garin Maiduguri, babban birnin jihar Barno daga Damaturu, sakamakon hare-haren Boko Haram a kan hanyar a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

Ana shiga Maiduguri ta hanyoyi shida ne, amma tun cikin 2014 aka datse sauran hanyoyi biyar din ba a bi ko shigowa birnin ta can, sai ta hanyar Damaturu kadai.

A can baya Boko Haram sun karya gadojin da ke hanyar bi a shiga Maiduguri, sai na kan hanyar Damaturu zuwa cikin Maiduguri ne kadai ba su samu nasarar karya ba.

Tun cikin 2014 sojoji da ‘yan sanda ke ta fama da Boko Haram, su na kokarin hana su karya Gadar Benishek, wadda ita kadai ce gada a tsakanin tafiyar kilomita 135, daga Damaturu zuwa Maiduguri.

Awowi 24 bayan haka kuma, sai suka bude wannan hanya. yanzu dai harkokin da tafiye-Tafiye ya dawo a wannan hanya.

Share.

game da Author