Sanatan dake wakiltan Kogi ta Yamma a majalisar dattawa Sanata Dino Melaye ya mika kansa ga ‘yan sanda a yau Juma’
Tare da sanata Dino akwai wasu daga cikin ‘yan uwan sa sanatoci da lauyan sa Mike Ozekhome tare dukkan su suka dunguma zuwa ofishin sufeto Janar din ‘Yan sanda Ibrahim Idris.
Sai dai isar su ke da wuya aka sanar dasu cewa Sufeton baya nan. Sai suka garzaya ofishin ‘Yan sandan SARS dake Abuja.
Yau Juma’a ne ya cika kwanaki 10 yana gida zagaye da ‘yan sanda.