Dattawan Barno na so a ba ’yan sanda bidigogi mai karfin harbo jirage

0

Dattawan Jihar Barno da suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata, sun nemi a dakatar da shirin gyaran dabi’un wadanda ake kira tubabbun ‘yan Boko Haram.

Sun ce wannan shiri da ake yi da sunan
‘Operation Safe Corridor’, ana sallamar tubabbun Boko Haram su na komawa cikin jama’a na zama hadari ga al’umman da suke garwaya da su.

Dattawan sun shaida wa Buhari cewa wannan shiri na haifar da sake yawaitar hare-hare a cikin jama’a.

Dattawan dai sun kai ziyarar ce a karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima, wanda a farkon lokacin da ya fara yi wa Buhari jawabi, aka ga ya barke da kuka.

Sun kuma nemi a wadatar da ‘yan sanda manyan bindigogin harbo jirage domin samun tunkarar ‘yan Boko Haram.

Sun kuma nuna rashin jin dadin yadda ba a turo dakarun CJTF dukabda suka rikida suka zama sojoji ba zuwa garin Maiduguri da sassan jihar dake fama da hare-kharen Boko Haram.

Sun ce idan da an shigar da CJTF cikin yaki da Boko Haram gadan-gaban, to za a samu gagarimar nasara, saboda sun san lunguna da sakon cikin jejin yankunan Barno.

Har ila yau, dattawan sun damka wa shugaba Buhari wasika mai dauke da bukatu 10 da suke so Buhari ya biya musu.

Wadannan dattawa sun shaida wa Bhari kamar yadda wani daga cikin su ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa dakarun CJTF da suka kware wajen kawo leken asiri, sun ce ‘yan Boko Haram din da ake saki bayan an yi musu rainon gyaran dabi’u, su ne kuma kan kai wa Boko Haram rahotanni.

Sun ce yawan hare-haren da Boko Haram ke kai wa a yanzu bayan sakin wasun su da sunan sun tuba, ya haifar da hare-hare na baya-bayan nan.

Sai suka kara yi wa Buhari tambihi da cewa ba a yi tunani ba kwata-kwata a batun kafa wannan shiri na gyara dabi’un ‘yan bindigar Boko Haram.

Tawagar ta kunshi tsoffin gwamnonin njihar biyu, sarakunan gargajiya, ‘yan majalisar tarayya da na jiha. Shugabannin kananan hukumomi, kungiyar Jama’atil Nasril Islam, CAN, ‘yan jarida da sauran kungiyoyi da dama.

Share.

game da Author