Wani abin da za a iya kira da abin al’ajabi da tashin hankali a gwamnatin Buhari shine yadda ake samun wadanda ke tare da shi kud da kud suna yi masa zagon kasa sannan suna caccakar gwamnatin sa yadda suke so.
A wani sabon faifai na radiyo da aka dauka a boye an ji ministan sufuri Rotimi Amaechi wanda shine darektan Kamfen din tazarcen shugaba Buharu yana hira da abokan sa inda ya ke cewa Najeriya fa ba ita bace take gaban Buhari ba.
” Shi fa Buhari ba ya daukar shawarar kowa abinda yake so ya ke yi, sannan babu abin da ya sha masa kai. Za ka iya rubuta duk abinda kake so abinka bai damu ba, domin ba karatu yake yi ba ma.Idan ma yaga ana sukar sa sai ya kira ka yace zo, zo ka gani wai zagi na suke yi, sai ya fashe da dariya abin sa.
” Akwai wani lokaci da muna tare a jirgin sama sai ya karanta labarin wani mai saida raguna a lokacin Sallah yana korafin rashin ciniki, cewa a gwamnatin Buhari babu kasuwa, sai Buhari ya kira ni ya ce in zo in gani, ko me ya hada shi da rashin saida ragunan sa a Onitcha da shi oho.
” Najeriya ba zata taba canja wa ba na rantse maka, idan ba kowa aka kashe ba kasarnan zata ci gaba da zama wuri daya ne cak.
Amaechi ya ce ya taba gaya wa sakataren gwamnatin sa a lokacin ya na gwamnan jihar Ribas cewa wannan kasar fa ta lalalce ba za ta taba gyaruwa ba.
” A lokacin Magnus Abe na sakataren gwamnatin jihar Ribas na taba gaya masa kasar nan fa ko kasata aka yi zuwa gida 10 kowa ya kama gaban sa ba za ta gyaru ba. A wancan lokacin ya rika cewa haba a matsayina na gwamna bai dace ina fadin haka ba sai gashi bayan ya zo Abuja da kan sa ya ce magana ta dutse.
Phrank Shuaibu, na kamfen din Atiku ne ya fidda wannan faifai da minista Amaechi ya zazzaro wadannan zantuka.
Phrank ya kara da cewa hakan ya dada tabbatar da irin kalaman da maidakin shugaban Kasa, Aisha Buhari ta rika cewa maigidanta ba shine ke gudanar da mulkin Najeriya ba, cewa wasu mutane ne da basu wuce uku ba suke yadda suka ga dama a kasar nan.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin Amaechi, kakakin sa David Iyofor ya ce suna nan suna ci gaba da bincikar wannan faifai domin samun tabbacin abubuwan da aka ce ministan ya fadi.