FARA SAKA DA MUBUN ZARE
Duk da cewa wasu kamfanonin kwangila kimanin 815 da ba su cika sharuddan karbar kwangiloli ba, amma duk da haka sai da Hukumar Inganta Al’ummar Kan Iyakokin Kasa (BDCA) ta rattaba sunayen su a cikin wadanda aka bai wa kwangiloli daban-daban.
Wannan ne karo na biyu da fallasa wannan hukuma da hannu dumu-dumu a cikin harkallar kwangilo.
Idan aka ce an rabbata sunan dan kwangila, to ana nufin an amince da aikin sa, kuma ya cika dukkan sharuddan da dokar karbar kwangila ta kasa ta gindaya.
Sai dai kuma wani jibgin takardun bayanan kwangila na Hukumar BDCA da PREMIUM TIMES ta yi nazari, wanda ya kunshi kwangilolin 2018 da ‘yan majalisar tarayya suka gudanar, kwata-kwata ba su cika mafi muhimmacin sharuddan da doka ta gindaya ba.
An dai buga tandar kwagilolin ne a cikin watan Agusta, 2018.
Hukumar ta tallata wasu ayyukan ‘yan majalisa kusan 400 wadanda duk wanda aka ba aiki, to a dare daya zai kudance. An saka ayyukan a cikin kasafin 2018.
Matsawar aka bar hukumomin BDCA suka gudanar da wannan karya dokar kwangiloli kai-tsaye, to duk wata kima da martabar yaki da cin hanci da rashawa ta fadi kasa warwas.
IYAR KWANGILAR KA IYAR SHAGALIN KA
Kwangilolin matsayi matsayi ce, kuma mataki mataki. Akwai masu ta naira milyan 10, wasu ma har ta naira milyan 200. Wato iyar kudin ka, iyar shagalinka kenan.
Ba wani ne shugaban wannan hukumar ba, sai surikin Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Junaid Abdullahi. An kafa hukumar cikin 2003, domin inganta rayuwar al’ummar da ke zaune a kan iyakokin kasar nan.
An dora mata nauyin gudanar da ayyukan raya karkara a jihohi 21, wadanda suka kunshi kananan hukumomi sama da 150.
GIWA TA FADI
An kafa kwamitin tantance ‘yan kwangilar da suka nemi aikin, wadanda kimanin su 987.
Jerin sunayen wadanda PREMIUM TIMES ta ci karo da su, sun kai 390, na wadanda aka amince da su yi aikin kwangilolin ayyuka kuma sayo kayayyaki a wurare daban-daban.
KA’IDOJIN KARBAR KWANGILA
Na farko an ce tilas sai kowane kamfani ya kawo rasidin shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku da suka gabata a jere.
Sannan kuma kada harkokin hada-hadar da kamfani ya yi ya kasance kasa da naira milyan 50 a cikin 2015, 2016 da kuma 2017.
Akwai kuma ka’idar cewa kowane kamfani sai ya kawo shaidar cewa ya bayar da takardar shaidar halartar horo na ITF da na NSITF.
An kuma rufe karbar tayin neman kwangila a ranar 1 Janairu, 2019.
WANCAKALI DA KA’IDOJI
Dama a baya PREMIUM TIMES ta taba bada labarin yadda aka yi watsi da ka’idojin bayar da kwangila a hukumar an shar’anta ka’idojin tun a doka ta 2007.
Doka ta shashe na 23(1) na 2007, ta ce babban laifin ne wata ma’aikata ko hukumar gwanatin tarayya ta karya sharuddan bayar da kwangila.
Sai dai kuma wannan duk bai shiga kunne hukumar ba, domin sun rika bin ka’idojin sun a karyawa.
FALLASA
Daga cikin kanfanoni 987, PREMIUM TIMES ta gano cewa 173 ne kacal suka cika sharudda.
Su kan su 173 din an gano cewa 13 daga cikin su ba su da takardun shaidar biyan haraji.
Ko su din ma da dam aba su da jarin naira milyan 50 da aka jujjuya a cikin shekarun 2015, 2017 da kuma 2017.
Wasu daga cikin kamfanonin da aka bai wa kwangilolin sun hada da:
1 – Aicon Residential Limited (Lot 84),
ABG Synergy Limited,
2 – Budmusdru Hill Nigeria Limited and Khamz Intercontinental,
3 – De Poor Shall Rich Nigeria Limited and Dankole Global,
4 – Yalele Farms Limited Equally,
5 – Al Nady Multi-Services Limited Constituency;
5 – Nitux Engineering Services Limited District, da kuma AIAG Energy Limited.
Kadan kenan daga cikin su. Daha wadanda aka ba kwangilar samar Keke NAPEF, sai wadanda aka ba kwangilar sayo ‘wilbro’ da sauran kayayyaki.
BA YAU NE FARAU BA
Ko a ranar 18 Ga Disamba, 2018, sai da PREMIUM TIMES ta fallasa ta fallasa yadda aka karya ka’ida wajen bayar da kwangiloli ga wasu kamfanoni 18 a Hukumar BDCA.
Wata kungiya mai suna CASEDA, ta yi kiran Kukumar BPE da ta duba lamarin wannan harkalla kuma a hukunta masu hannu a cikin ta.