Kwamishinnan ‘Yan Sandan Jihar Edo, Hakeem Odumosun, ya bayyana cewa wani dan sanda da aka bada rahoton an bindige a wani fada da ba san ko su wane ba, to dan kungiyar asiri ne.
Kwamishinan ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa fadan wanda aka yi a Benin, babban birnin jihar Edo, ya ci ran wasu ‘yan kungiyar asirin su biyu, baya ga na dan sandan.
NAN ta ruwaito cewa an bindige wani dan sanda mai suna Oisa Ehigie, a kan titin Normayo/Sakponba cikin Benin.
An kuma ruwaito cewa kisan na da nasaba da fadan ‘yan kungiyar asiri wanda ya sha cin rayuka da dama a Benin kwanan nan.
Kwamishinan ya ce dan sandan da aka kashe shi ma ya shiga fadan ne domin ya taya ‘yan bangaren sa, kuma ‘yan na sa bangaren ne biyu aka kashe tare da shi.
“Na je na gana da iyalin sa. Fada ne na kungiyar asiri, kuma shi ma dan kungiyar asirin ne.”Inji Kwamishinan ‘yan sandan na Edo.
Ya kuma ce an kama wasu mutane da ake zargi dangane da wannan kashe-kashen.