A kokarin kwantar da rikita-rikita da ya barke a gangamin taron PDP da aka yi a karamar hukumar Gwaram, jihar Jigawa tsautsayi ya fada kan wani cikin dubban magoya bayan jam’iyyar inda garin tattare mutane dan sanda ya dirka ma wani harsashi, nan take ya sheka lahira.
Hakan na faruwa kuwa sai jama’a suka hau wannan dan sanda da kila, inda ya samu ya tsira sai dai kuma hasalallun matasan sun rika bi suna banbanka wa motoci wuta.
A wannan taro dai an sami halartar tsohon gwamnan jihar Sule Lamido da dubban magoya bayan sa.