Dan majalisar Tarayya da ke wakiltar Kiyawa da Dutse jihar Jigawa, ya mika wa wasu ‘yan mazabar sa lasisin iya tuki har su hamsin.
Dan majalisar mai suna Ibrahim Kemba, ya bayyana cewa yayi haka ne domin samar wa mutanen jihar musamman wadannan mutane da ya samar wa lasisi gudanar da zirga-zirgar su a manyan titunan jihar ba tare da jami’an kiyaye haddura da na ‘Yan sanda suna muzguna musu ba.
A jawabin da yayi ya kara da cewa tabbas akwai wadanda za su kusa hadiye ran su saboda haushi da bakincikin ba su cikin wadanda aka ba, ina kira gare su da su yi hakuri su kwantar da hakalin su, suma nasu na na zuwa nan bada dadewa ba.
” Ina kira ga wadanda suka sami wannan lasisi da su gode wa Allah sannan su sani cewa ba wayon su bane ya basu Allah ne ya yi za su samu.
Wadanda aka ba wannan lasisi za du karbi ainihin katin shaidar bayan an kammala zabukan da za ayi a watannin Faburairu ne da Maris.
Bayan nan Kemba ya kaddamar da koyar wa mata sana’o’in hannu domin tallafa musu.
Mutane da dama sun tofa albarbacin bakin bisa wannan himma na Honorabul Kemba.
Da yawa sun ce yayi haka ne kawai domin neman kuri’un mutane amma ba wai don ya ga ya kamata ba.
” Wannan shine karo na biyu da yake wakiltar Kiyawa da Dutse a majalisar Tarayya amma saidai kaji shi jifa jifa, amma yanzu ya zo yana ta raba lasisi.” Inji wani Mazaunin Dutse.
Discussion about this post