DAN HAKIN DA KA RAINA: Yadda Solskjaer ya ceto Manchester United daga rami gaba dubu

0

Watanni biyu kenan bayan sallamar tsohon mai horaswar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, wanda aka maye gurbin sa da Ole Gunnar Solskjaer.

Solskjaer ba bakon suna bane a kunnuwan masu kallon kwallo a fadin duniyar nan, amma bakon suna ne a sahun manyan masu horas da kungiyoyin kwallo da suka shahara a duniya.

Shi ma tsohon dan wasan Manchester United din ne, wanda ta ke ji da shi, kuma ya na a sahun gaban taimaka wa kungiyar ta yi sharafin da har yau ba ta sake yi ba a duniya, a cikin 1999.

Sakwarkwacewar rikon igiyar da Mourinho ya rike Manchester United da ita, ta kawo kulob din ya shiga gararin da magoya bayan sa sun fara kaurace wa kallon wasa, saboda gudun bugawar zuciya da kuma hawan jini.

Daidai lokacin da karshen Mourinho ya kai makura, Manchester United ta kasance tamkar labule, duk kungiyar da ta bude, sai kawai ta shige ciki ta yi mata illa.

Maye gurbin sa da Ole Gunnar ya sanyaya wa magoya baya rai sosai, kuma ya dawo da martaba da karsashin kulob din da kuma musamman ‘yan kwallon sa.

Wasan sa na faro kwallaye hudu ya ci kuma ya yi nasara a matsayin sa na mai horas da kungiyar da ya taba buga wa wasa. Gunnar ya dore a haka, inda ta kai shi har ya buga wasanni shida a jere kuma duk ya na yin nasara.

Wasan da Manchester United ta buga da Tottenham a babban filin kwallon Landan a jiya Lahadi, ya nuna cewa Solskjaer ba bai abin na sa sa’a ba ce kadai, abin har ma da iya takun koyar da dabarun wasanni, wanda irin wannan dabarun ne suka subuce wa Mourinho a duk lokacin da Man United ta shiga filin kwallo.

Hakan ce ta sa shi babatu da hayagaga tsakanin sa da yaran da ya ke koyarwa, irin su Paul Pogba.

Farkon zuwan Solskjaer a Man United, ya zaburar da ‘yan wasan da su yi salon takun yawan fita ana kai hare-hare bagatatan. Wannan ce ta sa Manchester United ta rika cin kwallaye 3, 4 har zuwa 5.

A wasan ta na jiya da Tottenham kuwa, Solskjaer ya dankwafar da ‘yan bayan sa biyu masu yawan haurawa gaba su na tayawa a na kai hare-hare, wato Luke Shaw da kuma Ashley Young. Bai bar su sun rika kai hare-hare ba.

Harera da Nemanja Matic sun sauya taku, ba kamar lokacin Mourinho ba.

Nasarar da kungiyar ta samu a Tottenham har gida, ta nuna cewa Manchester da farfado. Abin da kawai ya rage ma ta, ta zarce da samun irin nasarar da take samu a yanzu, ko a wasannin ta na gida, ko a na waje, kuma ko da wace kungiya ce za su kafsa.

Wannan uzirin ne kawai magoya bayan kungiyar za a biya musu bukata da shi, domin su rika barci har da minshari bayan tashi daga wasa.

Share.

game da Author